Ruwa yana daga cikin abubuwan da muka fi amfani da su a rayuwa, amma abin mamaki shi ne: akwai abubuwa masu yawa da ruwa ke yi a jikinmu da mutane da dama basu sani ba. Ga jerin mahimman fa’idodi guda 10 da ruwa ke aikatawa a boye:
---
1. Ruwa Na Tsabtace Jikin Cikin Sauri
Ruwa yana taimakawa wajen fitar da gubobi da datti daga jiki ta fitsari da zufa. Wannan yana rage yawan kamuwa da cututtuka.
---
2. Yana Inganta Narkewar Abinci
Sha ruwa kafin ko bayan cin abinci yana taimakawa hanji ya motsa yadda ya kamata, yana magance toshewa da kumburi.
---
3. Yana Kara Hasken Fata
Ruwa yana sanyaya jiki daga ciki, yana ba fata ƙyalli, laushi, da kariya daga bushewa.
---
4. Yana Taimakawa Aikin Koda
Koda na tace gubobi ne, kuma ba za su iya yin aiki ba tare da ruwa ba. Rashin ruwa na iya jawo cututtukan koda.
---
5. Yana Inganta Aikin Zuciya
Idan jiki na da isasshen ruwa, jini yana gudana lafiya kuma zuciya na aiki ba tare da matsin lamba ba.
---
6. Yana Kare Kai Daga Ciwon Kai
Yawancin ciwon kai yana farawa ne saboda dehydrations (rashin ruwa). Sha ruwa yana magance hakan cikin mintuna kaÉ—an.
---
7. Yana Kara Kuzari
Rashin ruwa yana rage ƙarfin jiki. Idan ka sha ruwa, jikinka yana dawo da kuzari cikin sauri.
---
8. Yana Taimaka Cikin Rage Kiba
Ruwa na hana cin abinci da yawa saboda yana cika ciki, yana taimakawa wajen rage nauyi.
---
9. Yana Taimakawa Lungs (Huhu)
Ruwa yana kiyaye hanyoyin numfashi su kasance masu ruwa-ruwa, yana rage hadarin bushewar makogwaro da tari.
---
10. Yana Inganta Aikin Brain (Kwankwaro)
Kashi 70% na kwakwalwa ruwa ne. Idan ruwa ya ragu, hakan kan kawo mantuwa, gajiya, ko jinkirin tunani.
Ruwa ba kawai abin sha ba ne—magani ne, kariya ce, kuma sirrin lafiya. Ka tabbatar ka sha ruwa yadda ya kamata domin jiki ya yi aiki cikin inganci.
0 Comments