Bushewar lebe matsala ce da yawanci mutane ke fuskanta musamman a lokacin sanyi, iska, ko amfani da abubuwan shafawa masu ƙarfi. Rashin kula da lebe yana iya haifar da fashewar lebe, jin zafi, ko kuma fatar lebe ta yi ja. Ga wasu hanyoyi masu sauki da za ka bi domin samun lebe masu laushi da lafiya:
1. Shayar da Jiki Da Ruwa
Rashin ruwa a jiki yana sa lebe su bushe. Ka tabbata kana shan akalla kofi 8 na ruwa a rana. Hakanan, cin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa masu ruwa kamar kankana da ayaba zai taimaka.
2. Amfani da Lip Balm Mai Nourishing
Yi amfani da man lebe ko lip balm mai ƙunshe da sheanut butter, coconut oil, beeswax, ko vitamin E. Wannan zai taimaka wajen kare lebe daga bushewa da kuma gyara fatar da ta bushe.
3. Gujewa Lick Lebe
Yawan shafawa da harshen ruwa kan lebe yana cire mai na halitta da ke kiyaye lebe, wanda hakan na kara bushewa. Ka guji wannan dabi’a.
4. Exfoliate Lebe
Sau daya a mako, zaka iya amfani da toothbrush mai laushi ko sugar scrub domin cire fata ta bushe. Wannan zai sa lebe su zama masu laushi da haske.
5. Kare Lebe Daga Rana da Sanyi
A lokacin rana, amfani da lip balm mai SPF zai kare lebe daga hasken rana. A lokacin sanyi ko iska, shafa lip balm mai moisturizing zai rage bushewa.
6. Abinci Mai Amfani
Cin abinci mai vitamin A, C, E, da Omega-3 kamar kifi, avocado, kayan lambu masu kore, da almonds zai taimaka wajen kiyaye lebe da fata gaba daya.
Kammalawa
Maganin bushewar lebe yana bukatar kulawa daga ciki da wajen jiki. Shayar da ruwa, amfani da kayan moisturizing, da abinci mai gina jiki su ne hanyoyi mafi inganci domin samun lebe masu lafiya da laushi.
0 Comments