Sanyi yana iya janyo:
Tari
Mura
Ciwon kai
Zazzabi
Jin rauni da kasala
Akwai magungunan gargajiya da yawa da Allah Ya sanya a cikin tsirrai domin magance sanyi ba tare da illa ba.
---
🌿 Abubuwan Da Ake Bukata
1. 🧄 Albasa (garlic) – manyan guda 3
2. 🍋 Lemun tsami (lemon) – guda 2
3. 🍯 Zuma (honey) – cokali 3
4. 🌿 Kanumfari (cloves) – cokali 1
5. 🫚 Citta (ginger) – karamin yanki (grate)
6. 💧 Ruwa mai tsabta – kofi 2
---
🔥 Yadda Ake Hada Maganin
1. Tafasa ruwa: saka ruwa a tukunya ki tafasa shi.
2. Sanya kayan: bayan ruwa ya fara tafasa, sai ki saka albasa, citta, da kanumfari.
3. Bari ya tafasa na minti 10.
4. A tace ruwan: bayan ya huce ka ɗan tace.
5. Sanya zuma da lemun tsami: bayan ruwa ya ɗan huce, ka ƙara zuma da ruwan lemon tsami ka juya sosai.
---
☕ Yadda Ake Sha
A sha da safe kafin a ci abinci, da kuma da yamma kafin kwanciya.
A ci gaba da sha na kwana 3 zuwa 5, sai a daina idan sanyi ya lafa.
---
💪 Amfanin Wannan Hadi
Yana maganin mura da tari
Yana rage ciwon kirji
Yana karawa jiki ƙarfi
Yana ƙarfafa garkuwar jiki (immune system)
Yana maganin zazzabin sanyi (cold & flu)
---
⚠️ Lura:
Kada masu ciki su sha fiye da kofi ɗaya a rana.
Masu hawan jini su rage amfani da lemon sosai.
A tuntubi likita idan sanyi bai lafa cikin kwanaki 7 ba.
0 Comments