Idan kina zargin ciki, akwai hanyoyi biyu mafi sauƙi da kowa zai iya yi:
1️⃣ Home Pregnancy Test (PT Strip)
Kina iya saya a kowane pharmacy.
Yadda ake yi:
Fitar da fitsari a roba mai tsafta.
Saka strip ɗin a ciki na sekani 5–10.
Jira minti 2–5.
Sakamako:
Layuka 2 = Ciki
Layi 1 = Babu ciki
2️⃣ Gwajin Asibiti (Blood / Lab Test)
Wannan shi ne mafi inganci.
Yana gano ciki tun da wuri sosai.
Sakamako yakan fito cikin lokaci kaɗan.
Alamun farko da ake gani:
Jinkirin al’ada
Ciwo ko nauyi a ƙirji
Kasala ko bacci da yawa
Tashin zuciya (Morning sickness)
📝 Idan sakamakon ya rikita ki, ko kina da alamun amma PT ya nuna babu ciki — ki koma asibiti don a tabbatar
0 Comments