---
1. Taruwar Dattya da Gumi
Idan mutum ya dade ba ya yin wanka, datti da gumi suna taruwa a jiki. Wannan na sa wari, tsananin jin gajiya, da rashin jin daÉ—in kai.
---
2. Warin Jiki (Body Odor)
Kwayoyin cuta suna ƙaruwa a fata idan aka dade ba a wanka ba. Wannan ke sa wari mara daɗi wanda yake da wahalar ɓoyewa.
---
3. Fatar Jiki Ta Iya Yin Kuraje
Fatar jiki tana bukatar a wanke ta domin ta sami numfashi. Fashin yin wanka na kawo:
Kurajen fata
Rashin ƙosawa
Tsamin kai
Ƙaiƙayi
---
4. Zai Iya Haddasa Rashin Bacci
Mutanen da ba sa yin wanka kafin kwanciya na fama da rashin sassaucin jiki. Wanka na taimakawa ƙwaƙwalwa ta kwanta, ta rage stress.
---
5. Zubar Ciwon Kai da Rashin Walwala
Idan jiki ya cika da gumi da datti, jini baya yawo yadda ya kamata. Wannan kan haifar da:
Ciwon kai
Jin nauyi
Ƙarancin kuzari
---
6. Rashin Kyawun Fata
Idan aka yi watsi da wanka, fata na yin duhu, ta bushe, ta rasa laushi. Wannan kan sa mutum ya yi kama da wanda ya gaji sosai.
---
7. Zai Kawo Cutar Fata
Fasin yin wanka na iya jawo:
Fungus
Rashes
Fatar kafa ta fara wari
Athletes foot
---
8. Lalacewar Gashi
Gashi na bukatar tsafta kamar jiki. Taruwar mai da datti a kai na jawo:
Fatsar gashi
Gashin kai ya fara wari
Ƙaiƙayi da dandruff
---
9. Tashin Hankali da Stress
Fashin yin wanka na kara damuwa saboda jiki baya samun sabo da natsuwa. Wanka na rage matsin lamba, yana ba da nutsuwa.
---
Yadda Zaka Kare Kanka
Ka yi wanka aÆ™alla sau 1–2 a rana idan zafi ne.
Ka yi amfani da sabulun da ya dace da fatar ka.
Ka tsaftace kai da kyau bayan gumi ko aiki.
Ka tabbatar kana canza kaya masu datti.
Fashin yin wanka na iya zama abu mai sauƙi, amma yana iya kawo matsalolin lafiya da yawa. Ka riƙa yin wanka akai-akai domin kare kanka daga cututtuka, da jin daɗin jiki da kwanciyar hankali.
0 Comments